Philippines

Mutane Dubu 400 Sun Tsere Daga Gidajensu Sakamakon Fada A Philippine

Sama da mutane dubu 400 ne suka gudu suka bar garin Marawi da ke kudancin kasar Philippines, inda yanzu haka ake ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da kuma ‘yan tawaye.

Kusa da wani masallaci a garin Marawi na kasar Philippines inda ake ta artabu
Kusa da wani masallaci a garin Marawi na kasar Philippines inda ake ta artabu REUTERS/Romeo Ranoco
Talla

Tun ranar 23 ga watan mayun da ya gabata ne fada ta barke a wannan birni, wanda mafi yawan mazaunansa musulmi ne a cikin wannan kasa da ke da dimbin Kiristoci mabiya darikar Katolika.

Dakarun gwamnati na amfani ne da manyan makamai da suka hada da tankokin yaki da jiragen sama, domin yin luguden wuta akan ‘yan tawaye, yayin da wasu lokuta hare-haren ke shafar fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI