Japan

Ana Zabukan Kananan Hukumomi Mai Muhimmanci a Kasar Japan

Firaministan Japan Shinzo Abe
Firaministan Japan Shinzo Abe REUTERS/Thomas Peter

Al’ummar kasar Japan na jefa kuri'a yau Lahadi don zabukan kananan hukumomi wanda sakamakon zaben ke da muhimmanci a kasar inda Gwamnan Babban birnin kasar ke kalubalantar Jamiyyar Firaminista Shinzo Abe wanda farin jininsa ke raguwa.

Talla

Gwamnan Uwargida Yuriko Koike, wadda tsohuwar mai gabatar da shirye-shirye ce a tashan Talabijin na fatan ganin gamayyar jam'iyun da suka hada kai za su iya kawar da jam'iyar Firaministan dake mulki wato Jamiyyar Liberal Democratic Party, LDP.

Uwargida Yuriko Koike wadda aka zaba Gwamna a bara an sha fadin cewa tana da burin zama Firaministan  kasar Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.