Syria

Harin Kunar Bakin Wake a Syria ya Kashe Mutane Da Yawa

Inda aka sami harin kunar bakin wake a Syria
Inda aka sami harin kunar bakin wake a Syria REUTERS/Firas Makdesi

Rahotanni  daga kasar Syria na cewa mutane da yawan gaske ake kyautata zaton sun mutu yau Lahadi sakamakon wani mummunar harin kunar bakin wake a gabashin yankin birnin Damascus.

Talla

Majiyoyin samun labarai na cewa jami'an tsaro sun kama wasu motoci uku dauke  bama-bamai  lahadi da safe, nan take kuma biyu suka tarwatse.

Mota ta uku kuma ita ma sai da jama’a aka kewayeta  ta tarwatse.

Wasu alkaluma daga bisa na cewa akalla mutane tara suka mutu, wasu kimanin 15 kuma suka jikkata.

Rami Abdel Rahman na kungiyar dake sa idanu kan wainar da ake toyawa a Syria na cewa cikin mamatan akwai fararen hula da kuma Sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI