Israel
An Sallami Tsohon Firaministan Israela Olmert Daga Gidan Sarka
Wallafawa ranar:
Da safiyar yau Lahadi ne Hukumomin kasar Isra'ila suka saki tsohon Firaministan kasar Ehud Olmert daga gidan yari a wani afuwa da aka yi masa kafin ya yi rabin wa’adin zama gidan kaso da aka diba masa.
Talla
Ya kasance na farko cikin Shugabannin kasar da aka daure a gidan sarka, kuma bayan sallaman na sa ya ki ce uffan ga manema labarai.
Dan shekaru 71 ya yi Firaministan ne tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2009.
A watan Fabarairu na shekara ta 2016 aka bankado ya taba cin hanci da rashawa kuma aka zartar masa da hukuncin dauri na tsawon watanni 27.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu