Sahel - Faransa

Shugaban Faransa Macron na Ziyara a Mali Yau

Shugaba  Emmanuel Macron tare da shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta yayin ziyara a Gao na kasar Mali ranar 19  Mayu  2017.
Shugaba Emmanuel Macron tare da shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta yayin ziyara a Gao na kasar Mali ranar 19 Mayu 2017. RFI

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyara a kasar Mali yau Lahadi a kokarin da kasar sa ke yi don marawa kasashe biyar na yankin Sahel baya su yaki masu ikirarin jihadi da 'yan ta'adda a yankunan.

Talla

Kasashen biyar da suka hada da Nijar, Burkina Faso, Mali, Chadi da Mauritania sun lashi takobin kawar da masu ayyukan ta’addanci da masu jihadi dake yankin kasashen su, kuma kasar Faransa ta bayyana bada nata gudun mawa.

Emmanuel Macros zai shiga taron shugabannin kasashen biyar da za su yi a Bamako inda zai bayyana irin gudunmawar da za su samu.

Dakarun hadin guiwa na kasashen biyar mai cibiya a garin Sevare dake tsakiyar Mali na da Dakaru dubu biyar don shiga sauran Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su dubu sha biyu da suka hada da na Faransa dubu hudu dake yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.