Amurka

Trump ya fitar da bidiyo yana dambe da CNN

Trump ya doke kafar CNN
Trump ya doke kafar CNN Capture d'écran Twitter

Shugaban Amurka Donlad Trump, ya yada wani hoton bidiyo a twitter inda ya ke nuna kansa yana dukan wani mutum da aka rufe fuskarsa da tambarin kafar yada labarai ta CNN.

Talla

Wannan dai wata alama ce da ke nuni da cewa shugaban na matukar adawa da kafafen yada labarai, da ya ke zargi da nuna masa kiyayya tun daga lokacin yakin neman zabensa har zuwa yau.

Donald Trump ya fitar da wannan hoton bidiyo ne a shafinsa na Twitter kwanaki uku bayan da ya fito ya yi kakkausar suka ga kafafen yada labarai, wadanda ya ce sam ba sa kaunar shi.

A wata sanarwar da ta fitar a matsayin martani, kafar talabijin ta CNN ta bayyana wannan hoto da cewa tamkar shugaban yana kira ne da aka kai wa ‘yan jaridu hari, kuma ko kadan hoton bai dace da shekaru da matsayinsa na shugaban kasa ba.

Hoton bidiyo na tsawon mintuna 28, ya nuna Trump ya shake wani dan kokuwa da ya rufe fuskarsa da tambarin tashar ta talabijin ta CNN, daga nan kuma ya ci gaba da noshinsa har sai da ya kwantar da shi a kasa.

Daga karshen dai a cikin bidiyon an ji shugaban na cewa, "FNN", da ke nufin Fraud News Network, wato tashar talabijin mai yada labaran karya.

Asalin hoton dai an dauke shi ne kimanin shekaru 10 da suka gabata lokacin da Trump ke gabatar da wani shirin talabijin a matsayinsa na mai ruwa da tsaki a wasan kokawar da ta yi fice a kasar Amurka da ake kira "Wresttling’’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI