Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai cin dogon zango

Hukumomin Rasha da China a yau talata sun yi kira zuwa kasar Koriya ta arewa don gani hukumomin kasar sun mutunta ka’idoji dangane da batun nukliyar ta, banda haka Rasha da China sun bukaci Amurka ta dakatar da atisayi da take gudanar a wasu tsibiran yankin asiya.

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzame mai cin dogon zango
Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzame mai cin dogon zango Wikimedia Commons/US Navy
Talla

Kasar Koriya ta arewa a yau talata ta sake gwajin makami mai lizame,wanda hakan ke a matsayi sabuwar tsokana a idanu Amurka.

Yan lokuta da sanar da samu nasarar gwajin ,kasashen Duniya sun soma nuna fargaba,an dai bayyana cewa makami ya ci kimani kilometa 2.802.

Masu sharhin kan batutuwan da suka shafi tsaro na hasashen cewa kasar Koriya ta Arewa ta mallaki karfin da ya dace wajen kai hari zuwa kasar da take so a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI