Amurka na son a tsaurara takunkumi akan Koriya ta Arewa
Wallafawa ranar:
Amurka tare da goyon bayan Faransa za ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da wani daftarin kuduri, domin sanya sabbin takunkumai a kan Koriya ta Arewa, sakamakon gwajin makami mai linzame da ta yi ranar talata, daidai lokacin da Amurka ke gudanar da bukukuwar ranar ‘yancin-kai.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Nikki Haley, ta bayyana gwajin makamai wanda zai iya fadawa a jihar Alaska idan har Koriya ta harba shi, a matsayin wanda zai iya kai ga barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu.
Amma Rasha ta ce ba za ta goyi bayan sabon kudurin ba, yayin da China ke cewa ba za ta bari lamarin ya kai ga yin amfani da karfin soji ba.
Jekadan Amurka ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa idan amfani da karfi ya kama dole za su iya daukar matakin domin magance barazanar Koriya ta arewa.
Amurka na son China ta ci gaba da matsin lamba ga aminiyarta Koriya domin ta jingine shirinta na mallakar makamin nukiliya.
Ana sa ran shugaban China Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump za su tattauna da juna a taron G20 a Jamus da za a gudanar a karshen mako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu