US-EU

''Makomar kasashen yammaci na cikin hatsari''

Shugaban Amurka Donald Trump na rangadi a Turai
Shugaban Amurka Donald Trump na rangadi a Turai REUTERS/Kacper Pempel

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nuna cikakken goyon bayansa ga kungiyar tsaro ta NATO adai-dai lokacin da ya soma rangadi a Turai tare da gargadi makomar kasashen yammaci wanda ya bayyana cewa na cikin hatsari.

Talla

Mista Trump da yanzu haka ya isa birnin Hamburg da ke Jamus, ya kuma zargi Rasha da yin kafar angulu a zaman lafiyar duniya.

Donald Trump na Amurka da ya yi jawabi a birnin Poland kafin ya wuce kasar Jamus ya gargadi cewa rashin hadin-kai ba karamin tasiri yake yi tsakanin kasashen da ke kawance da juna da kuma bude kofa ga yakin cacar baka.

Shugaban ya ce kare yammaci ba wai abune da za ake dauka sakwa-sakwa ba domin magana ce ta tabbatar da wanzuwar al’ummar kasashen.

Trump ya ci gaba da cewa, akwai alaka me karfi tsakanin Amurka da Turai wanda yake fatan dorewarsa.

Sai dai shugaban ya soki Moscow, kwana guda su hadu da shugaban Vladimir Putin na Rasha a taron G20, tare da yin tir da yadda kasar ke da halin yin kafar angulu.

Trump ya ce ba bu abin mamaki Moscow ta yi kokarin taka rawa a zaben kasar na 2016 da ya bashi mulki, sai dai tayi hakan ne da taimakon wasu tare da daura laifi kan magabancinsa Barack Obama da gaza daukan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.