G20

Zanga-zangar adawa da taron G20 ta koma rikici

Masu zanga-zanga sun kone motocin 'Yan sanda a  Hamburg
Masu zanga-zanga sun kone motocin 'Yan sanda a Hamburg REUTERS

‘Yan sanda 76 ne suka samu raunuka a lokacin da suke kokarin kwantar da tarzomar da masu adawa da taron shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da za a soma a yau Juma’a a birnin Hamburg na kasar Jamus suka yi a cikin daren da ya gabata.

Talla

Har zuwa safiyar Juma’a an ci gaba da yin artabu tsakanin masu adawa da manufofin taron da kuma jami’an tsaron da aka jibge a cikin shirin ko-ta-kwana.

Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun toshe hanyoyi a Hamburg kafin soma taron.

Daruruwan mutane ne da ke nuna adawa da manufofin jari hujja suka shiga zanga-zangar, wadda da farko ta lumana ce kafin daga bisani ta rikide zuwa tarzoma, inda masu zanga-zangar suka yi amfani da duwatsu da kuma kwalabe suna jifar jami’an tsaro.

An bayyana adadin wadanda suka shiga zanga-zangar da cewa zai kai mutane dubu 12, kuma wasu daga ciki sun share tsawon kwanaki suna gudanar da gangami a kan titunan birnin na Hamburg kafin lamarin ya rikide zuwa tarzoma a cikin daren jiya.

Sama da ‘yan sanda dubu 20 ne aka jibge domin tabbatar da tsaro a lokacin taron. Sai dai ana hasashen cewa sama da mutane dubu 100 ne za su fito domin yin zanga-zanga a tsawon kwnaki biyu da za a share ana gudanar da taron.

Tuni dai shugabannin manyan kasashen duniya suka isa birnin Hamburg domin taron na yini biyu, wanda zai mayar da hankali kan batun matsalar dumamar yanayi da kuma ayyukan ta’addanci, yayin da taron zai kasance dama domin yin ganawar farko tsakanin Donald Trump na Amurka da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.