MDD

Manyan kasashe sun ki amincewa a haramta makamin nukiliya

Masu fafutika sun bukaci ra ufe cibiyoyin nukiliya a duniya
Masu fafutika sun bukaci ra ufe cibiyoyin nukiliya a duniya ®Wikipedia

Kasashe 122 na duniya sun amince da kudirin wata yarjejeniyar duniya da za ta haramta amfani da makaman nukiliya, a yayin da kuma manyan kasashe kamar Faransa da Birtaniya da Amurka suka yi watsi da matakin musamman a yanzu da suke fuskantar barazanar Koriya ta arewa.

Talla

Kudirin ya samu amincewar kasashe 122 a zauren Majalisar Dinkin Duniya, amma babu wata kasa daga cikin kasashe 9 a zaman taron da suka mallaki makaman nukiliya wadanda suka hada da Amurka da Rasha da China da Faransa da Birtaniya da Isra’ila da Koriya ta Arewa da India da kuma Pakistan.

Kasar Japan ma ta kauracewa zauren Majalisar wacce aka taba kai wa hari da babbar makami a 1945.

An kwashe makwanni ana tattauna kudirin a Majalisar Dinkin Duniya wanda ya kunshi inganta shirin nukiliya da barazanar amfani da makamin.

Yawancin Kasashen Latin Amurka da Afrika ne suka amince a haramta amfani da makamin da kuma kasashen Iran da Iraqi.

Jekadun Amurka da Faransa da Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya sun ce babu wani mataki na magance barazanar Koriya ta Arewa da kundin kudirin yarjejeniyar ke kunshe da shi.

Manyan kasashen dai sun ce makaman da suka mallaka na nukiliya na kariyar kai ne daga duk wata barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI