G20

Putin da Trump sun yi ganawar keke da keke

Vladimir Putin na Rasha tare da Donald Trump na Amurka a Hamburg gefen taron G20
Vladimir Putin na Rasha tare da Donald Trump na Amurka a Hamburg gefen taron G20 REUTERS/Carlos Barria

Shugaba Donald Trump na Amurka da Vladimir Putin na Rasha sun yi ganawar farko ta keke da keke kan batun zargin katsalandan da Rasha ta yi a zaben shugabancin Amurka.

Talla

Manyan Shugabannin kasashen biyu na duniya sun gana ne a gefen taron kasashe 20 masu karfin tattalin arzikin duniya G20 da ake gudanarwa a birnin Hamburg na Jamus.

A tattaunawar dai shugaba Putin ya musanta zargin da ake wa Rasha, kuma sakataren harakokin wajen kasar Sergei Lavrov ya ce shugaba Trump ya aminta da abinda Putin ya fada.

Sauran batutuwan da shugabannin suka tattauna a ganawar ta sama sa’o’I biyu sun hada da batun rikicin Syria da yaki da ta’addanci.

Ganawar shugabannin kasashen biyu na zuwa a yayin da kasashen suka amince a tsagaita buda wuta a kudu masu yammacin Syria daga gobe Lahadi.

Rasha da Amurka sun amince a tsagaita buda wutar a yankin Daraa da Quneitra da Sweida da kuma yankin Golan Height na Isra’ila inda ta taba mayar da martani kan fadan da ‘Yan tawaye da dakarun Gwamnatin Syria suka gwabza a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.