G20

Zanga-zanga ta mamaye taron G20 a Hamburg

Masu zanga-zanga na adawa ne da tsarin jari hujja a duniya
Masu zanga-zanga na adawa ne da tsarin jari hujja a duniya REUTERS/Hannibal Hanschke

Shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arzikin duniya G20 sun shiga rana ta karshe a taron da suke gudanarwa a Hamburg na Jamus da ke fuskantar zanga-zangar dubban mutane.

Talla

Batutuwan da ake sa ran za su mamaye taron a yau rana ta karshe sun hada da fahimtar manufofin Donald Trump na Amurka musamman batun cinikayya da kuma canjin yanayi bayan ya yi watsi da yarjejeniyar Paris.

Zanga-zangar adawa da taron na G20 na ci gaba da kazancewa a Hamburg inda aka rahotanni suka ce ‘yan sanda su yi harbi sama domin tarwatsa masu zanga-zangar.

‘Yan sanda sun nemi karin jami’an tsaro a Hamburg sakamakon arangamarar da suke yi da masu zanga-zangar.

Rahotanni sun ce matar Donald Trump na amurka ta yi lattin isa taron matan shugabannin kasashen na G20 da wuri bayan masu zanga-zangar sun hana ta fita a gidan da ta sauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.