Amurka

Amurka ta ware kanta kan dumamar yanayi a taron G20

Friministan Canadá, Justin Trudeau da Donald Trump na Amurka da kuma Shugaba Michel Temer na Brazil a taron G20
Friministan Canadá, Justin Trudeau da Donald Trump na Amurka da kuma Shugaba Michel Temer na Brazil a taron G20 REUTERS/LUDOVIC MARIN

Shugabannin kasashen G20 masu karfin tattalin arziki a duniya, sun cim-ma daidaito a kan dukkanin batutuwan da taronsu ya tattauna a kai, sai dai Amurka ta ware kanta a yarjejeniyar rage dumamar yanayi.

Talla

Taron da aka gudanar a birnin Hamburg na Jamus, shugabar gwamnatin kasar Angela Markel, ta ce ta cim-ma burinta na shawo kan mahalarta taron kan batun kasuwanci da kudadde da makamashi da kuma Afirka.

Kana kasashen sun kuma amince da ficewar Amurka daga yarjejeniyar ta birnin Paris, Sai dai hakan ba zai hanasu aiki tare da Amurkan ba, wajen aiwatar da wasu daga cikin tsare tsaren rage dumamar yanayin, idan bukatar hakan ta taso.

Wani jami’I da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, shugabannin kasashen na G20 sun kai kimanin karfe biyun dare, kafin kammalla taronsu a jiya Assabar ana kokarin gani ko Donald Trump na Amurka zai aminta da tsare-tsaren tunkarar rage dumamar yanayi.

A watannin baya ne Mista Trump ya bayyana ficewar Amurka daga yarjejeniyar da aka cim-ma kan matsalar sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.