Amurka

Dan Trump ya taba ganawa da Lauyan Rasha

Dan shugaban Amurka da ake kira Donald Trump karami
Dan shugaban Amurka da ake kira Donald Trump karami REUTERS

Dan shugaban Amurka Donald Trump ya amsa cewa ya gana da wata lauya ‘Yar kasar Rasha inda suka tattauna kan ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton.

Talla

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar dan shugaban ya gana da lauyar ‘Yar kasar Rasha a bara domin karbar bayanan asiri kan Hillary Clinton.

Dan shugaba Trump ya ce lalle ya gana da lauyar Natalia Veselnitskaya amma babu wasu bayanan kirki da ya samu kan Clinton.

Rahotanni sun ce an yi ganawar ne a ranar 9 Yunin shekarar 2016 bayan tabbatar da Donald Trump a matsayin dan takarar jam’iyyar Republican a zaben shugaban kasa

Cikin wadanda suka halarci ganawar har da Jared Kushner, surikin shugaba Trump da kuma tsohon shugaban yakin neman zabensa Paul J Manafort.

Hukumomin Amurka dai na kan bincike domin tabbatar da ko Trump ya hada baki da Rasha domin yin katsalandan a zaben shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.