Amurka

Hana tafiya da na’urar komfuta daga wasu tashoshin jiragen sama 4 zuwa Amurka

Jirgin sama
Jirgin sama

Hukumomin kasar Amurka sun ce har yanzu an haramtawa wasu tashoshin jiragen sama 4 barin matafiya su tashi da na’urar komfuta zuwa Amurka saboda kaucewa barazanar tada bama bamai.

Talla

Ma’aikatar tsaron cikin gida ta bayyana wadannan tashoshi da suka hada da filin jiragen saman Riyadh da Jeddah dake Saudi Arabia da kuma na Alkahira da Casablanca dake Masar da Morocco.

Ma’aikatar tace an cire filaye 6 dake Gabas ta Tsakiya daga haramcin da aka dora a watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.