Brazil

Lula da Silva zai sha daurin shekaru 9 da rabi

Tsohon shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva
Tsohon shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva REUTERS/Paulo Whitaker

Wata Kotu a Brazil ta yankewa tsohon shugaban kasar Inacio Lula da Silva hukuncin daurin shekaru 9 da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin cin hanci da rashawa da halarta kudaden haramun.

Talla

Kotun ta ce ta gamsu da shaidun da aka gabatar mata na irin kudaden da tsohon shugaban ya karba daga kamfanin man kasar Petrobras da kuma cin hancin da 'yan kwangila suka bashi.

Alkalin kotun ya ce tsohon shugaban na da hurumin daukaka kara.

Shugaba Lula da ya mulki Brazil tsakanin shekarar 2003 zuwa 2010 ya bunkasa tattalin arzikin kasar inda ta zama daya daga cikin kasashen da arzikin su yafi habaka a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.