Amurka-China

China ta kare kanta daga zargin Amurka

harakokin hada-hada a kasar China
harakokin hada-hada a kasar China REUTERS/Lucy Nicholson/

Hukumomin China sun fitar da wasu rahotani a wani mataki na kare kai daga zargin Amurka na cewa sun keta takunkuman da aka kakabawa Koriya ta arewa tareda ci gaba da hulda ta kud da kud da kasar.

Talla

China ta bayyana cewa tun a ranar 18 ga watan Fabrairu shekarar bana ne ta dakatar da tura gawayi zuwa koriya ta arewa, sai dai wasu rahotani dake karo da juna ,sun tabbatar da cewa an samu karin cinikaya tsakanin China da Koriya ta Arewa na kusan kashi 10 da dugo 5 cikin dari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.