CUBA

Shugaba Castro ya soki matakin Shugaba Trump

Shugaban kasar Cuba Raul Castro
Shugaban kasar Cuba Raul Castro

Shugaban kasar Cuba, Raoul Castro a jiya juma’a ya soki matakin Shugaban Amurka Donald Trump na kawo sauyi kan matsayar da kasashen biyu suka cimma a lokacin tsofuwar Gwamnatin Obama.

Talla

Shugaban Cuba ya danganta yanayin diflomasiyar kasashen biyu da ci baya.

A shekara ta 2015 tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci sake dawowa da hulda tsakanin Cuba da Amurca, tun bayan yanke duk wata hulda da wannan kasa a shekara ta 1959.

A karshe shugaba Raoul Castro ya bayyana cewa Gwamnatin Trump na kokarin yawo da hankalin yan kasar Cuba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI