Qatar-Saudiya

Faransa ta bukaci magance rikicin kasashen Larabawa

Faransa ta bukaci Qatar da kasashen Larabawa da su dauki matakan rage tankiyar da ke tsakaninsu domin ganin an dinke barakar da aka samu. Ministan Harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana haka a ziyarar da ya kai kasashen da ke Yankin da zimmar shiga tsakani.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian tare da takwaransa na Saudiya  Adel al-Jubeir a birnin Riyad.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian tare da takwaransa na Saudiya Adel al-Jubeir a birnin Riyad. AFP
Talla

Ministan Le Drian a ziyarar da ya kai Abu Dhabi ya ce, yana da matukar muhimmanci kasashen da ke wannan rikici su tattauna a tsakaninsu domin ganin an bude kofar warware matsalar.

Le Drian wanda ya yaba da rawar da Kuwait ke takawa wajen shiga tsakani, ya ce Faransa ba za ta so a sauya matsayin na Kuwait ba, sai dai za ta taimaka wajen ganin an samu nasara.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana takaicinsa da barakar da aka samu tsakanin kasashen, in da ya yi kiran kawo karshensa cikin gaggawa.

A ziyarar da ya kai a yankin, Minista Le Drian ya gana da Yariman Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed al Nahyan da Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad Al Sabah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI