Amurka

Farin jinin Trump na kara raguwa a Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Wani bincike ya nuna cewa farin jinin shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da raguwa sakamakon irin matakan da ya ke dauka wajen tafiyar da kasar musamman soke shirin inshoran lafiyar ta Obamacare.

Talla

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Jaridar Washington Post da kuma tashar talabijin ta ABC suka gudanar, ta nuna cewa, kasa da watanni shida bayan kama aiki, farin jinin shugaba Donald Trump ya ragu daga kashi 42 a watan Afrilu zuwa 36 a yanzu.

Rahotan ya ce, kashi 48 na mutanen da aka tuntuba sun ki amince wa da rawar da shugaban ke takawa, sabanin rawar da shugabanin da suka gabata irin su Bill Clinton da Barack Obama da kuma George Bush suka taka.

Wasu kashi 48 kuma, sun bayyana damuwarsu ganin yadda karfin shugabancin da Amurka ke da shi a fadin duniya ke raguwa, saboda jagorancin Trump.

Wasu kashi 66 sun ce, ba su gamsu da yadda shugaba Trump ke tattaunawa da shugabannin kasashen duniya ba, musamman shugaban Rasha Vladimir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI