JAMUS

An yi wa yara 547 fyade a makarantar Katolika ta Jamus

Majami'ar Regensburger ta Jamus ta kai kimanin shekaru dubu 1 da assasa ta
Majami'ar Regensburger ta Jamus ta kai kimanin shekaru dubu 1 da assasa ta facebook.com/regensburgerdomspatzen

Akalla kananan yara 547 ne aka ci zarafinsu ta hanyar yi mu su fyade ko kuma azabtar da su a wata makarantar mabiya darikar Katolika ta horar da mawakan Majami’a a Jamus.

Talla

Bayanin na kunshe ne cikin wani rahoton bincike da aka fitar a ranar Talata, wanda aka dauki tsawon lokaci ana gudanar da shi kan zargin da ake na lalata yara a makarantar horar da mabiya darkar katolikan da ke birnin Bavaria a kudancin kasar.

Tun a shekarar 2010 ne, makarantar da ke amsa sunan Regensburger Domspatzen, mai shekaru kimanin dubu daya, ta tsunduma cikin zargin tafka ta’asar wadda ta karade majami’u darikar katolika a sassan duniya.

A lokacin da ya ke bayyana sakamakon karshe na binciken da ya gudanar, lawya mai zaman kansa Ulrich Weber ya ce, ya samu shaidun da ke bada tabbacin bata akalla yara 67, yayin da wasu 500 suka fuskanci cin zarafi ta hanyar azabtarwa, a tsakanin shekarun 1945 zuwa 1990.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa, kawo yanzu, an gano wadanda suka aikata laifukan a wancan lokacin guda 49, ko da ya ke ba a sa ran za a hukunta su saboda tsawon lokacin da aka dauka, sai dai za a biya dukkanin wadanda suka fuskanci cin zarafin diyyar Euro dubu 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI