Amurka-Rasha

Shugaba Donald Trump ya gana da Vladmir Putin ta bayan fage

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque

Fadar Shugaban Amurka tace sau biyu shugaba Donald Trump ya gana da shugaba Vladimir Putin na Rasha a wajen taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki da akayi a Hamburg dake Jamus.

Talla

Wani jami’in fadar shugaban Amurka yace bayan takaitacciyar ganawar da suka yi wajen fara taron na kwanaki biyu da kuma ganawar sa’oi biyu da suka yi, shugabannin sun kuma tattauna da Putin a daren karshe na taron.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda shugabanin biyu suka tattauna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.