Blackberry

WhatsApp ya toshe a wayoyin Blackberry

Sai karshen shekara WhatsApp ai toshe a wayoyin Blackberry
Sai karshen shekara WhatsApp ai toshe a wayoyin Blackberry Allan White/ Fotos Públicas

Masu amfani da Blackberry da dama sun bayyana damuwa kan yadda shafinsu na WhatsApp ya daina aiki a rana tsaka a yau Laraba duk da cewa kamfanin na WhatsApp ya tsawaita wa’adin da ya diba na daina aiki da wasu nau’in wayoyin salula da suka kunshi har da Blackberry.

Talla

Masu amfani da Blackberry da dama a Najeriya sun ce sun wayi gari a yau WhatsApp din su ya daina aiki, inda mutum ba zai iya karba da aika sako ba.

Da dama sun dauka cewa wa’adin da WhatsApp ya dauka ne ya cika a yau Laraba 19 ga watan Yuli.

A watan jiya ne WhatsApp yasanar da tsawaita wa’adin da ya ba wayoyin Blackberry kirar OS da suka kunshi Z10 da Curve da kirar Nokia S40 da suka kunshi Asha da X2 da C3 da kuma Lumia 520 zuwa karshen watan Disemban bana.

Tun a karshen watan Yuni WhatsApp ya daina amfani da woyoyi kirar Nokia S60 da kuma sauran wayoyi masu amfani da tsohon tsarin Android.

Sai dai kuma binciken da RFI Hausa ta gudanar ta gano cewa masu amfani da tsohon tsarin WhatsApp ne ya toshe musamman ga masu amfani da Blackberry.

Akwai bukatar a sabunta tsarin na WhatsApp wato Update idan har ana son ci gaba da amfani da shafin kafin cikar wa’adin.

Tun a watan Maris na 2016 ne WhatsApp ya sanar da dakatar da aiki ga kirar wayoyin Blackberry, matakin da masu amfani da kamfanin suka kaddamar da yekuwa a shafukan intanet inda aka kirkiro shafin #ILoveBB10Apps a twitter domin nuna adawa da WhatsApp.

Daga baya dai WhatsApp ya tsawaita wa’adin zuwa watan Yunin 2017 kafin ya sake tsawaitawa zuwa karshen shekarar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI