Amurka

Kotu ta sake yin tarnaki ga shirin hana baki shiga Amurka

Kotun Kolin Amurka ta sake yin tarnaki ga shirin shugaba Donald Trump na haramtawa baki daga wasu kasashen Musulmi izinin shiga kasar, inda kotun ta ce dokar ba ta shafi kakanin masu zama a kasar ba da jikokin su.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Wannan hukunci ya nuna cewar, kotun ta amince da matsayin wata kotun Hawaii na makon jiya, wadda ta cire ‘yan uwa na kusa da mutanen da ke zama a kasar ta Amurka daga umurnin.

Kotun ta ce wannan matsayi na wucin gadi ne har sai an kammala shari’a kan daukaka karar da gwamnatin Amurka ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI