Amurka-Ta'addanci

‘‘An samu raguwar hare-haren ta’addanci a duniya’’

Amurka ta ce an samu raguwar hare haren ta’addancin a shekarar 2016
Amurka ta ce an samu raguwar hare haren ta’addancin a shekarar 2016 AFP/Dimitar Dilkoff

Amurka ta ce an samu raguwar hare-haren ta’addancin da ke kai wa ga rasa dimbin rayuka a shekarar 2016, sakamakon raguwar harin da ake samu a kasashen Afghanistan da Syria da Najeriya da Pakistan da kuma Yemen.

Talla

Rahotan da ma’aikatar cikin gidan Amurka ta fitar ya ce an samu raguwar hare-haren ta’addanci a bara da kashi 9 na irin hare-haren da aka gani a shekarar 2015, yayin da adadin mutanen da harin ke ritsawa da su ya ragu da kasha 13.

Alkaluman da jami’ar Maryland ta tattara sun nuna cewar an samu hare-hare 11,072 a fadin duniya bara, abinda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 25,600, kuma cikin wannan adadi 6,700 maharan ne.

Rahotan ya ce an samu hare-haren ne a kasashe 104 bara, amma akasarin su sun fi yawa ne a kasashe biyar da suka hada da Iraqi da Afghansitan da India da Pakistan da kuma Philippines.

Kana kashi Uku bisa Hudu na mace-macen da aka samu sun fi yawa ne a Iraqi da Afghanistan da Syria da Najeriya da kuma Pakistan.

Rahotan ya yaba da irin ci gaban da aka samu a Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.