Amurka

Watanni 6 na Trump: Ko shugaban ya cika alkawuransa?

Shugaban Amurka Donald Trump ya cika watanni shida kan karaagar mulki.
Shugaban Amurka Donald Trump ya cika watanni shida kan karaagar mulki. REUTERS/Yuri Gripas

A yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya cika watanni shida akan karagar mulki, hankulan manazarta sun karkata ne kan cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa ko kuma akasin haka.

Talla

A yayin yakin neman zabensa, shugaba Donald Trump ya yi alkawarin gina Katanga akan iyakar Mexico don dakile kwararar baki cikin kasarsa.

Sai dai wannan buri nasa bai cika ba duk da cewa, ya bada umarnin assasa katangar da ya ce, Mexico ce za ta biya kudi gina ta, kana, bai samu goyon bayan Majalisa ba wajen gina katangar da aka kiyatsa cewa, za ta laukme Dala miliyan dubu 20.

A ranar 1 ga watan Yunin wannan shekarar, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar dumamar yanayi ta birnin Paris kamar yadda ya alkawaranta a yakin neman zabensa.

Trump ya sha alakanta wanann yarjejeniya da shiririta.

A game da alkawarinsa na soke tsarin inshorar lafiya ta Obamacare kuwa, ana iya cewa, burin shugaban ya gamu da nakasu, domin kuwa a cikin wannan makon ne, shirin ya wargaje bayan mambobin jam’iyyarsa ta Republican a Majalsar kasar sun ki kada kuri’ar amincewa da sabon ishorar lafiya da za ta maye Obamacare da tsohon shugaba Barrack Obama ya samar.

A game da alkawarinsa na hana daukacin Musulmai shiga Amurka kuwa, Donald Trump ya cika wani bangare na wannan alkawarin, in da kotun koli ta amince wa dokarsa ta wucen gadi kan hana Musulman Iran da Somalia da Sudan da Syria da Yemen shiga kasar, amma fa ga wadanda ba su dangi a Amurka.

Har ila yau, burin Mr. Trump na sake cimma yarjejeniyar Nukiliyar Iran da kawo karshen mayakan ISIS bai cika ba duk da alkawarin da ya yi akansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.