Amurka

An yi wa O.J Simpson na Amurka afuwa

O.J. Simpson a lokacin da aka yanke ma sa hukuncin zaman gidan yari a Las Vegas a shekarar 2008
O.J. Simpson a lokacin da aka yanke ma sa hukuncin zaman gidan yari a Las Vegas a shekarar 2008 (Photo : Reuters)

An yi wa tsohon dan wasan kwallon kafa a Amurka O.J Simpson afuwa bayan ya shafe tsawon shekaru 9 a gidan yari saboda samun sa da aikata laifin fashi da makami a wani otel da ke Las Vegas a shekarar 2007.

Talla

Wasu mambobi 4 na kwamitin afuwa na jihar Nevada da ke kudancin Amurka ne, suka kada kuri’ar yin afuwa ga Simpson mai shekaru 70.

Ana saran sakin Simpson don ci gaba da rayuwa a cikin al’umma nan da ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

A can baya dai, an wanke tsohon dan wasan daga zargin kashe matarsa shekaru 20 da suka gabata bayan an dauki lokaci ana zaman sauraren shari’a, in da daga bisani aka gaza samun shaidun da za su tabbatar da laifin da ake zargin sa da aikatawa.

Shari’ar tsohon dan wasan ta dauki hankulan jama’a a Amurka da kuma sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.