MDD

Yaki da cutar kanjamau ya ci karo da matsaloli a shekarar bara

Shirin yaki da cutar kanjamau
Shirin yaki da cutar kanjamau ARIS MESSINIS / AFP

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce adadin masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV-Aids ko SIDA na karuwa a sassan duniya, yayin da masu fama da cutar ke fuskantar halin rashin tabbas kan magungunan rage kaifinta.

Talla

Rahoton wanda sashen kula da cutar na MDD ya wallafa a ranar Alhamis, ya nuna cewa cutar ta lakume rayukan miliyoyin mutane a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ce ba wadanda suka mutu ko masu fama da cutar ne ke fuskantar kalubale ba har ma da dubban wadanda ke karbar kulawar kariya daga cutar inda masana su ka yi gargadin cewa dole ne a kara kaimi wajen samar da magungunan rage kaifin cutar.

A cewar rahoton mutane milyan 19 da dubu 500 ne cikin sama da milyan 36 da ke fama da cutar a duniya suka samu damar shan maganin rage kaifin cutar a shekarar 2016, wanda kuma shi ne karon farko da kusan rabin masu fama da cutar suka gaza samun magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI