Ukraine

Kawo karshen rikicin Ukraine

Shugaban Ukraine Petro Porochenko da shugaban zartarwa na kungiyar tarrayar Turai
Shugaban Ukraine Petro Porochenko da shugaban zartarwa na kungiyar tarrayar Turai REUTERS/Valentyn Ogirenko

Fadar Shugaban Faransa ta bayyana shirin shugabanin kasashen Jamus, Rasha ,Ukraine da ita Faransa na wata tattaunawa ta wayar talho ranar litinin domin kawo karshen rikicin Ukraine.

Talla

A wannan tattaunawa za su mayar da hankali zuwa rikicin kasar Ukraine kamar dai yada aka shata a tattaunawar watan fabrairu sheakarar 2015.

An dai kwashe kusan shekaru uku ana ci gaba da kai ruwa rana a rikicin Ukraine da ya lakume rayyukan mutane kusan 10.000.

Hukumomin Ukraine da kawayenta na turai na zargin Rasha da dafawa yan aware dake kokarin wargaza zamana lafiya da aka cimma a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.