Afghanistan-Amurka
Sojin Amurka sun kashe 'yan sandan Afghanistan 16
Wallafawa ranar:
Sojin saman Amurka sun kai hari tare da kashe ‘yan sandan kasar Afghanistan 16, bisa zaton cewa mayakan Taliban ne.
Talla
Lamarin ya faru ne a yankin Helmand, a daidai lokacin da ‘yansanda suka kai samame domin murkushe wani gungu na mayakan Taliban, inda sojin saman na Amurka suka yi masu barin bisa zaton cewa ‘yan sandan magoya bayan Taliban ne.
A daya bangare kuwa wasu ‘yan bindiga sun yi awun gaba da mutane 70 daga wani kauye a yankin Kandahar na kasar ta Afghanistan, kuma ana zargin ‘yan Taliban da aikata haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu