Indonesia
Shugaban Indonesia Ya Umarci A Harbe Masu Safarar Kwayoyi
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo ya umarci ‘yan sandan kasar da su bindige har lahira duk wani dillalin miyagun kwayoyi da suka nemi kama shi ya ja da su.
Talla
Joko Widodo na bada wannan umarni ne a jawabinsa wajen taron jam'iyar siyasa inda ya nemi yan sanda da su ga lallai an taimaka wajen yakin da yake yi da dillalan miyagun kwayoyi.
Yana mai cewa su sa idanu sosai kan baki dake shiga kasar da miyagun kwayoyi, kuma idan har an kama mutun ya nemi turjiya to a bindige shi nan take.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu