Turkiya- Saudiya- Qatar

Shugaban Turkiya Ya Tafi Saudiya Saboda Sasanta Rikicin Kasashen Larabawa

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayip Erdogan na shirin fara wata ziyara ta kwanaki biyu a kasar Saudiya yau Lahadi domin tattauna yadda za’a kawo karshen rikici tsakanin manyan kasashen Larabawa hudu da kuma kasar Qatar.

Shugaban Turkiya Erdogan tare da Sarki Salman na Saudiya
Shugaban Turkiya Erdogan tare da Sarki Salman na Saudiya RFI
Talla

A yau ake sa ran Shugaban Turkiya ya sauka a Saudiya inda zai gana da Sarki Salman na Saudiya, kafin ya tafi kasar Kuwait wadda take shiga tsakani daga nan kuma  ya tafi kasar Qatar.

Ya fadi bayan sallar Juma’a shekaranjiya cewa zai ga lallai an warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin kasashen na Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI