MDD

MDD na tattauna sabon rikicin Isra'ila da Falasdinu

Sabon rikicin ya barke bayan Isra'ila ta hana Falasdinawa masu kasa da shekaru 50 shiga Masallacin Kudus domin gudanar da ibada.
Sabon rikicin ya barke bayan Isra'ila ta hana Falasdinawa masu kasa da shekaru 50 shiga Masallacin Kudus domin gudanar da ibada. REUTERS/Ronen Zvulun

A wannan litinin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na zama na musamman domin tattauna sabon rikicin da ya barke tsakanin Falasdinawa da Isra’ila sakamakon hana wadanda shekarunsu suka haura 50 shiga masallacin Kudus don yin ibada.

Talla

Tuni dai shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sanar da katse duk wata hulda da Isra’ila sakamakon wannan mataki da kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.

Shugaba Abbas ya kuma fara aiwatar da wannan barazana ta hanyar kaurace wa wani taron samar da tsaro tsakin Falasdinu da Isra’ila wanda kafin barkewar wannan rikici aka tsara gudanarwa a jiya lahadi.

Sakamakon sabbin matakai da Isra’ila ta dauka a masallacin na Kudus, kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 10, Falasdinawa 7 da kuma Yahudawa 3, yayin da wasu da dama suka samu jikkata.

Wasu daga cikin matakan da Yahudawan suka dauka sannan kuma ke ci gaba da kara fusata Falasdinawan, sun hada da kafa kemarorin daukar hoto da kuma na’urorin da ke gano wanda ke dauke da karfe a jikinsa a kowanne sashe na masallacin, yayin da aka jigbe wasu daruruwan sojoji da ‘yan sanda a kan hanyoyin da ke sada sauran unguwanni da masallacin.

Yayin da kowanne daga cikin bangarorin ke ci gaba da tsayawa kan matsayinsa, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirin gudanar zama don tattauna wannan batu a birnin New York na Amurka a wannan Litinin, kamar dai yadda kasashen Masar da Faransa da kuma Sweden suka bukaci a yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI