Libya

Libya ta cimma matsayar tsagaita wuta da 'yan tawaye

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Firaministan Libya Fayez al-Sarraj a hannun hagu da kuma Khalifa Haftar a hannun dama
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Firaministan Libya Fayez al-Sarraj a hannun hagu da kuma Khalifa Haftar a hannun dama REUTERS

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, Fayez al-Sarraj da kuma janar Khalifa Haftar wanda ke rike da muhimman yankunan kasar, sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da soma shirye-shiryen gudanar da zabubuka a kasar nan ba da jimawa ba.

Talla

Taron wanda mutanen biyu suka gudanar a birnin Paris karkashin jagorancin shugaban Fransa Emmanuel Macron, ya kasance na farko da daya daga cikin manyan kasashen duniya ta dauki nauyin shiryawa a baya-baya nan.

A cewar Macron, za a iya gudanar da zabuba a kasar ta Libya kafin karshen shekara ta 2018, to sai dai kafin nan, dole ne a tabbatar da cewa an tsagaita wuta a tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai a sassan kasar a cewarsa.

Sanarwar da mutanen biyu suka sanyan hannu ta kunshi batutuwa guda 10, da suka hada da tsagaita wutar, sai kuma tabbatar da cewa an hana yaduwar makamai a cikin Libya, wanda shi ne sharadin farko don share fagen gudanar da zabuka.

Libya dai na fama da yakin basasa ne tun a shekara ta 2011, bayan da ‘yan tawaye tare da samun goyon bayan manyan kasashen duniya suka kashe shugaban kasar Kanar Mu’ammar Gadhafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.