Rasha-China

Rasha da China na atisayen farko a tekun Baltic

A karon fako kenan da China da Rasha ke gudanar da atisayen soji a tekun Baltic
A karon fako kenan da China da Rasha ke gudanar da atisayen soji a tekun Baltic ABIMATA HASIBUAN / AFP

China da Rasha na gudanar da atisayen soji irinsa a karon farko a tekun kasashen yankin Baltic a wani yunkuri na karfafa tsaro da sake gina rundunar kasashen biyu a duniya. Sai dai atisayen ya gamu da suka daga kasashen Baltic da Poland da suka ce, ana shiga iyakokinsu ba tare da neman izini ba.

Talla

Tun a shekarar 2012, Rasha da China ke gudanar da atisayen hadin-gwiwa,  yayin da a shekarar da ta gabata, suka yi amfani da tekun kudancin China, wanda Beijing ke takaddama akai da kasashe biyar da suka hada iyakokin tekun.

Kasashen sun gudanar da  atisayen 2015 a tekun Baharu-rum, a dai-dai lokacin da Rasha ke fuskantar matsi kan rawar da ta ke takawa a rikicin Ukraine, kana Moscow ke shirin daukan matakan soji a Syria.

Sai dai atisayen yau Talata, na zuwa ne bayan aike sojin ruwan China a karon farko cikin shekaru 60  zuwa sassanin Djibouti, a ci gaba da fadada ayyukanta na bada tsaro a duniya.

Jiragen yakin China 3 da kuma 10 na Rasha, hade da jirage masu saukan angulu, ake amfani da su wajen atisayen.

China ta shiga atisayen ne da daya daga cikin jiragenta na zamani samfurin O52D destroyer, wanda ta kaddamar a cikin Disamba 2015, dauke da makamai mazu linzami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.