kimiya

An kusa daina amfani da motoci masu aiki da man fetir

Nan da shekarar 2040 ne ake saran yawaitar motoci masu amfani da wutar lantarki
Nan da shekarar 2040 ne ake saran yawaitar motoci masu amfani da wutar lantarki cleantechnica.com

Kasashen duniya da suka ci gaba ta fannin kimiyya da fasasha na ci gaba da bayyana shirinsu na kera motoci masu amfani da wutar lantarki, abin da zai kawo karshen motocin da ke amfani da man fetir ko kuma dizil.

Talla

A wannan Laraba ne, Birtaniya ta sanar da shirinta na kawo karshen siyar da motocin da ke amfani da man fetir da dizil nan da shekarar 2040, bayan Faransa ta sanar da makamancin matakin a cikin wannan wata da zimmar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

A bara ne dai, China ta gabatar da nata shirin da ya bukaci siyar da kashi 12 cikin 100 na motoci da ke amfani da batir nan da shekarar 2020.

Ita ma India ta ce, nan da shekarar 2030 ne ta ke fatan fara amfani da motoci masu aiki da wutar lantarki.

Kazalika, kasar Norway na da irin wannan burin na kawo karshen siyar da motoci masu aiki da man fetir nan da shekarar 2025, kamar yadda su ma Sweden da Denmark da Finland duk suka sanar da irin wannan shiri.

A dalilin yunkurin wadannan kasashe ne, wani Farfesa kan ilimin kimiya da fasasha a Jami’ar York, Alastir Lewis ya yi hasashen cewa, nan da shekarar 2040, injinan kananan motoci masu fitar da hayaki za su bace da kansu ba tare da gwamnati ta tabuka wani abu ba.

Sai dai wasu masana na ganin cewa, matakin zai yi illa ga kasashen da suka dogara da mai don samun kudin shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI