Faransa-Africa

Faransa za ta gina cibiyoyin tantance bakin haure a Libya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Pascal Rossignol

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da aniyar gina cibiyoyin tantance bakin hauren da ke shirin tsallakawa Nahiyar Turai a Libya cikin shekarar nan. Matakin da shugaban ya sanar a yau Alhamis na daga cikin yunkurin da ake na ganin an samu raguwar yan ciranin da ke kwararowa kasashen Turai.

Talla

Cibiyoyin tantance Yan-ciranin a cewar Shugaba Macron za su taimaka wajen tantance adadin mutanen da suka cancanci a basu damar zamowa yan gudun hijira a kasashen Turai.

haka kuma cibiyoyin za su taimaka rage yawan mutanen da ke fadawa hadari a kokarin su na shiga Nahiyar Turai musamman ta hanyar amfani da kasar ta Libya da ke matsayin kan iyaka.

A lokacin da ya ziyarci cibiyar tsugunar da yan gudun hijira ta Orieans da ke tsakkiyar kasar, Shugaba Macron ya ce ko ba da sahalewar kungiyar tarayyar Turai ba zai tarbi mutanen da ke jefa kansu a cikin hatsari don ganin sun shiga nahiyar.

Macron ya bayyan cewa zai aika da tawagar hukumar da ke kula da yan gudun hijira ta Faransa l'Ofpra ga sansanonin tsugunar da bakin hauren kasar Italiya,inda kuma ya sanar da mataki sake samar da makamantan cibiyoyin tantancewar a Jamhuriyyar Nijar.

Macron ya ce rayuwar da kimanin mutane dubu 800.000 ke a karakashin rumfuna a kasar ta Libya ya saba da mutuntukar dan adam inda kuma ya yi fatan ganin Libyan ta farfado daga halin da ta ke ciki a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.