Amurka-Iran
Amurka ta sanya wa Iran takunkumi
Wallafawa ranar:
Amurka da wasu kawayenta na nahiyar Turai sun bukaci Iran da ta dakatar da shirinta na gwajin duk wani makami mai linzami.
Talla
Wannan na zuwa ne bayan Tehran ta harba roka mai kunshe da tauraron dan adam a matsayin gwaji, abin da Amurka ta bayyana a matsayin tsokana.
A wata sanarwa hadin gwiwa da suka fitar, Birtaniya da Faransa da Jamus duk sun yi tarayya da Amurka wajen fadin cewa, gwajin da Iran ta yi ya saba wa dokokin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
A jiya Jumma’a ne, Amurka ta kakaba takunkumi ga Iran bisa gwajin makamin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu