Amurka

Trump ya nada sabon shugaban ma'aikatansa

Shugaba Donald Trump tare da  John Kelly, sabon shugaban ma'aikata a fadar White House
Shugaba Donald Trump tare da John Kelly, sabon shugaban ma'aikata a fadar White House REUTERS/Mike Segar

Shugaban Amurka Donald Trump ya nada sakataren tsaro a ma’aikatar cikin gidan kasar, Janar John Kelly a matsayin sabon shugaban ma’aikatan Fadar House White, in da ya maye gurbin Reince Priebus, da ke cikin tsaka mai wuya.

Talla

Mr. Trump ya sanar da nadin ne a shafinsa na Twitter bayan sabon Darektan sadarwarsa, Anthony Scaramucci ya caccaki Priebus kan zargin sa da fallasa wasu bayanan sirri ga ‘yan jarida.

A hirar da ya yi da kafar Talabijin ta CNN, Mr. Priebus ya ce, tun a ranar Alhamis ya yi ritaya daga mukaminsa bayan wata ganawa da ya yi da shugaba Trump.

Priebus ya kara da cewa, shugaba Trump ya zabi wata hanya daban kuma ya bayyana Janar Kelly a matsayin kwazo.

Shi ma Trump ya ce, Janar Kelly na da kishin Amurka kuma babban jagora ne.

A ranar Litinin mai zuwa ne ake saran Mr. John Kelly zai kama aiki a fadar White House.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.