Amurka-Koriya

Amurka ta kera makamin da zai kakkabo makaman Koriya

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai sau 14
Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai sau 14 OLIVIER FOURT/RFI

Amurka ta ce ta yi nasarar gwajin wani makami da ta kera da zai iya kakkabo makamai masu linzami wanda kuma za ta girke a yankin Koriya. Wannan na zuwa bayan koriya ta arewa ta sake yin nasarar gwajin wani makami mai linzami.

Talla

Amurka ta ce makaminta da ake kira THAAD na cin matsakaicin zango ne wanda aka yi nasarar gwajinsa a yankin Alaska, kuma karo na 15 ke nan ana gwajin makamin domin tabbatar da ingancinsa.

Za a girke makamin ne a yankin Koriya ta kudu domin tunkarar barazanar Koriya ta arewa.

A ranar Juma’a ne Koriya ta Arewa ta gudanar da gwajin babban makami mai linzame da ta ce gargadi ne ga Amurka da ke kokarin ganin an sake kakaba ma ta takunkumi.

Koriya ta arewa ta yi gwajin makamin ne da ke cin dogon zango da zai iya shiga Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.