Venezuela

Ana Zabukan Sabbin Wakilan Majalisar Kasar Venezuela Yau

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela rfi.

Alummar kasar Venezuela na gudanar da zabukan wakilan Majalisar Dokokin kasa su  545 yau lahadi duk da boren gamagari da ake ta yi a fadin kasar.

Talla

Shugaba Nicolas Maduro ya bayyana cewa akwai nasara a zaben da ake yi  wanda ake ganin zai kawo karshen rinjaye na wakilai 'yan adawa a majalisar.

‘Yan adawa  sun bayyana kauracewa zaben na yau.

Kasashen Amurka, da kasashen kungiyar Turai, da kasashen latin America duk sun soki zaben na yau.

Watanni hudu ke nan ake ta bore a fadin kasar kuma mutane akalla 100 suka rasa rayukansu sakamakon tarzoma da ake samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.