Venezuela

An harbe wani dan takara a Venezuela

'Yan sanda na arangama da masu zanga-zanga a Caracas
'Yan sanda na arangama da masu zanga-zanga a Caracas REUTERS/Carlos Garcia Rawlins

A yayin da ake gudanar da zaben ‘yan majalisu a Venezuela mai fama da rikici da matsalolin tattalin arziki, rahotanni sun ce an kashe daya daga cikin ‘yan takarar dan majalisa.

Talla

Jose Felix Pineda, wanda lauya ne kuma daya daga cikin wadanda ke gwagwarmayar sake rubuta kundin tsarin mulki, an kashe shi ne a gidansa da ke garin Bolivar kafin soma kada kuri’a.

Ana zaben ne dai cikin yanayi na fargaba da tashin hankali a Venezuela inda wasu rahotanni suka ce an kashe shugaban matasa ‘yan adawa a wani gangani adawa da zaben da ake gudanarwa a yau Lahadi.

An shafe kwanaki ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin Nicolas Maduro, inda mutane sama da 100 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.