Pakistan

Majalisar Dokokin Pakistan Za Ta Zabi Firaminista Ranar Talata

Shahbaz Sharif wanda shine kani na tsohon Firaministan Pakistan Nawaz Sharif
Shahbaz Sharif wanda shine kani na tsohon Firaministan Pakistan Nawaz Sharif RFI

Majalisar Dokokin  Pakistan za ta zabi sabon Firaministan kasar ranar Talata sakamakon sauke tsohon Firaminista Nawaz Sherif da kotun kololuwa ta kasar ta yi saboda samunsa da laifin cin hanci.

Talla

Jam’iyar dake mulki ta sanar da cewa kani na tsohon Firaministan Shahbaz Sharif na iya maye kujerar yayansa amma kuma sai dole ya shiga majalisar Dokoki ta hanyar tsayawa takarar kujeran tsohon Firaministan.

A halin da ake ciki Kungiyar Pakistan Muslim League- Nawaz, PML-N wadda take da rinjaye a Majalisar Dokokin  ta sanar da cewa ta gabatar da tsohon Ministan albarkatun man fetur Shahid Khaqan Abbasi domin zama Firaminista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI