Isa ga babban shafi
Amurka

Ana ruguguwar ficewa Florida kafin isowar guguwar Irma

Guguwar Irma ta isa Cuba tafe da iska mai karfi da ruwan sama.
Guguwar Irma ta isa Cuba tafe da iska mai karfi da ruwan sama. REUTERS/Alexandre Meneghini
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Dubban mutane ne ke ruguguwar ficewa Florida a Amurka kafin isowar mahaukaciyar guguwar Irma da yanzu haka ta isa Cuba dauke da iska mai karfi da ruwan sama.

Talla

Guguwar Irma ta isa Cuba bayan ta yi barna a wasu tsibaran yankin Caribbean.

Guguwar da aka ce yanzu ta kai rukuni na biyar na gudu ne a kilomita 190.

Guguwar ta tsallake Bahamas ta fada Cuba.

Amurka ta bukaci mutane Miliyan 6 su kaurace a yayin da guguwar ta doshi Florida.

Akalla mutane 20 suka mutu sakamakon guguwar musamman a tsibiran Caribbean da ta fara yin barna a tsakanin Alhamis zuwa jiya Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.