Isa ga babban shafi
Jamus-Najeriya-Portugal

'Yan Sandan Jamus Sun Fasa Garken Masu kulla Auren Jabu Tsakanin Maza 'Yan Najeriya Da Mata Yan Portugal

Shugaban Najeria Muhammadu Buhari da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel yayi wata ziyara da Buhari ya kai Jamus.
Shugaban Najeria Muhammadu Buhari da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel yayi wata ziyara da Buhari ya kai Jamus. RFI
Zubin rubutu: Garba Aliyu
Minti 1

‘Yan Sanda a Jamus sun fasa garken wasu ‘yan danfara dake kulla auren karya tsakanin mata ‘yan kasar Potugal da maza ‘yan Najeriya domin samun takardun izinin zama a kasashen Turai.

Talla

‘Yan Sandan Jamus sun bayyana cewa suna tsare da mutane biyar da suka hada da mata hudu a lokacin da aka kai samame a wurare 40 dake sassan kasar Jamus.

Majiyoyi sun bayyana cewa dubban kudade ake kashewa wajen auren zamba.

Masu bincike sun bayyana cewa masu kulla irin wannan aure kan dibo mata daga kasar Portugal, yayin da  ake karban dubban kudade daga 'yan Najeriya domin kulla aure da ‘yar Portugal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.