Bakonmu a Yau

Dr Aliyu Hong: Tasirin taron Majalisar Dinkin Duniya karo 72

Sauti 03:34
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump yayin ganawar da suka yi a taron majalisar dinkin duniya a birnin New York.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump yayin ganawar da suka yi a taron majalisar dinkin duniya a birnin New York. LUDOVIC MARIN / AFP

YAU ake fara taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 inda ake saran shugabannin kasashen duniya 193 zasu gabatar da jawabai daban daban kan yadda za’a inganta majalisar da kuma magance matsalolin da suka addabi kasashen duniya. Dangane da batun maganar sake fasalin Majalisar da kuma fadada kwamitin sulhu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Dr Aliyu Idi Hong.