Amurka

Amurka za ta tallafawa musulmi 'yan kabilar Rohingya

Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya ne yanzu haka suka samu matsugunai a wani sansani da ke gab da birnin Cox's Bazar na Bangladesh, September.
Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya ne yanzu haka suka samu matsugunai a wani sansani da ke gab da birnin Cox's Bazar na Bangladesh, September. Reuters

AMURKA na shirin bai wa musulmi ‘yan Kabilar Rohingya da ke kasar Myanmar wadanda yanzu haka su ke gudun hijira a Bangaladesh tallafin kudi da suka kusa Dalan Amurka Miliyan 32. Wata sanarwa da Ma'aikatar wajen kasar ta fitar ya ce ta sanar da hakan, inda ta ce halin musulmin ke ciki abin a tallafa musu ne.

Talla

Sanarwan ta ci gaba da cewa da tallafin ya kunshi na samar da wuraren kwana da  abinci, da ruwan sha, da ma sauran muhimman abubuwan bukatu na jama’a sama da dubu 400 da aka tarwatsa daga Myanmar suka shiga Bangladesh don tsira da rayukansu.

Bayanai dai na nuna cewa mutane sama da dubu 400 wadanda suka zarce rabin al’ummar Rohingya ne suka bar gidajensu ba shiri cikin makonni uku da suka gabata sakamakon rikicin addinin daya barke a kasar.

An dai yi zargin dakarun Gwamnatin Myanmar da aikata kisan gilla ga tsirarun musulman 'yan kabilar Rohingya ba gaira babu dalili, lamarin daya tilasta musu barin matsugunansu tare da neman mafaka a makwabciyar kasar Bangaladesh.

Yanzu haka dai Bangladesh ce ke ci gaba da daukar dawainiyar 'yan gudun hijirar da yawansu ya haura mutum dubu 400 inda kuma ta yi alkawarin gina musu gidaje a sabon sansani da aka bude masu.

Sakataren harkokin wajen na Amurka Rex Tillerson a wannan mako ya gana da jagoran Myanmar Aung San Suu Kyi inda kuma ya bukaci da ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta kawo karshen muzgunawa musulmin kabilar ta Rohingya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.