Myanmar

Myanmar na shirin maido da 'yan Rohingya gida

Mutanen Rohingya da ke fakewa a Bangladesh sakamakon rikicin jihar Rakhine ta Myanmar
Mutanen Rohingya da ke fakewa a Bangladesh sakamakon rikicin jihar Rakhine ta Myanmar REUTERS/Cathal McNaughton

Gwamnatin Myanmar ta ce, a shirye ta ke ta fara kwaso ‘yan kabilar Rohingya daga Bangladesh domin mayar da su gida, a dai-dai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da yi wa mahukuntan kasar matsin lamba.

Talla

Ministan Harkokin Wajen Bangladesh Mahmood Ali, shi ne ya sanar cewa sun samu tabbacin hakan daga wakilan gwmanatin Myanmar, a dai-dai lokacin da adadin ‘yan Rohingya da suka tsallaka zuwa kasar ya kai dubu 800.

Ganawar Ministan da wakilan Myanmar karkashin jagoranci takwaransa na kasar Kyaw Tint Swe, na zuwa ne bayan ziyarar da wakilan Majalisar Dinkin Duniya suka kai Jihar Rakhine a karon farko tun soma tashin hankalin.

Sai dai Ministan bai bada lokacin komawar ‘yan gudun hijirar ba kuma babu tabbacin ko mutane dubu dari 300 da suka tsere daga yankin tun rikicin farko na cikin wadanda za a maida kasar.

Shugabar gwamnatin Mynamar Suu Kyi, wacce ke fuskantar Suka saboda gazawarta wajen samar da zaman lafiya a jihar, ta ce Myanmar za ta mayar da ‘yan gudun hijirar Rohingya da aka tantance.

Suu Kyi ta ce, za ta bi tsarin dokokin da aka amince da shi a 1993, lokacin dawo da dubban ‘yan Rohingya da suka bar kasar.

Kungiyoyin agaji na ci gaba da bayyana furgabarsu kan halin da dubban al’ummar Rohingya ke ciki wadanda ke bukatar abinci, magunguna da matsugunai cikin gaggawa, la’akari da yadda rikicin ya tagayyara yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.