Amurka

'Yan Sanda na binciken musabbabin harin Las Vegas

'Yan Sandan Amurka na binciken musabbabin harin birnin Las Vegas
'Yan Sandan Amurka na binciken musabbabin harin birnin Las Vegas David Becker/Getty Images/AFP

Jami’an ‘yan sandan Amurka sun dukufa wajen gano dalilin da ya tinzira wani mutun har ya kai harin bindiga a birnin Las Vegas, in da ya kashe mutane akalla 59 tare da jikkata 527 a wani gidan rawa.

Talla

Stephen Paddock mai shekaru 64 ya bude wutar ne daga hawa na 32 na Otel din Mandalay Bay da ke kusa da gidan rawar, in da jama’a ke shagalin bikin kade-kade da raye-raye a yammacin ranar Lahadi.

Jami’an ‘yan sanda sun gano bindigogi 23 a dakin da maharin ya karba a Otel din Mandalay Bay, baya ga wasu tarin makamai daban da aka gano a gidansa da ke jihar Nevada.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da musabbabin kaddamar da farmakin.

Masu bincike sun ce, maharin ba shi da wata alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya duk da ikirarin kungiyar ISIS.

Sai dai wasu daga cikin masu binciken na ganin cewa, watakila akwai dalilai masu nasaba da lafiyar kwakwaluwa da suka tinzira maharin.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kazamin harin a matsayin tsan-tsan mugunta, kuma ana saran zai kai ziyarci Las Vegas a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.